MA'ANAR CRYPTO CURRENCY


 


Kamar yadda muka sani kalmar Crypto asalin ta kalmar Girkawa ne (Greek Word) tana nufi "Secret" ko "Hidden" abin nufi "Sirranchewa" ko "Rufaffewa" daga nan aka samo kalmar Crypto da ma'anar ta, dalilin da yasa aka bawa kudin Online wannan suna shine saboda tsarin yadda aka shirya kimiyyar gudanar dashi akan wani tsari da ake ce wa "Block Chain Technology" ko "Kimiyyar da take jere akan tsari hawa-hawa kamar bulo".

Click here

Tsarin Crypto Currency, yana kan abinda ake ce ma Block Chain Technology ne, shi kuma block chain Technology tsari ne na Database, duk wanda yasan me ake kira da database toh zai yi saurin fara hasaso wannan kimiyyar ta Block Chain.

Database wuri ne ko tsari ne da ake ajiye bayanai, da tattara su wuri guda ko a rarrabe, tare da canza su ko gyara su a lokacin da ake bukata.

.

Tsarin database yana da yawa, yafi guda 40 a bangaren masu ilimin Computer, akwai Distributed database, akwai Relational database, akwai Centralized, akwai decentralized, akwai Cloud da sauran su.

Toh shi Block Chain Technology yana kan tsarin Decentralized distributed ledger ne, sai dai tsarin sa yasha ban ban da asalin tsarin database ta wasu wurare, shi Block Chain Technology an tsari ne ta yadda ba'a iya canza bayanan dake cikin sa da zaran an shigar, kuma ba'a iya sace shi, ko hacking din sa ko ayi masa kutse saboda tsaron da aka saka masa.

.

Har yau an gagara samun wani ko wasu kwararrun hackers da suka iya hacking din Block Chain Technology, ba'a samu ba, hatta wadanda suka fi kowa kwarewa a harkar Internet da suke kasar Switzerland da Japan da Uruguay sun sadakar chewa ba zasu iya komaiwa Block Chain Technology ba, wato ginin Mahdi ka ture kenan.

Shi Block Chain Technology baya karban komai sai dai dai da tsarin sa, toh idan ya karba kuma babu wanda zai iya dakatar dashi har wanda ya kirkiro tsarin.


Haka zai yi ta tafiya duniya tana amfana dashi Koda masu shi sun mutu ko sun watsar dashi.

Misali;-

 koda wanda ya kirkiro Bitcoin yace ya fasa ya daina, toh a yau ba zai iya dakatar dashi ba, sai dai ya hakura.

Haka kuma tsarin Block Chain Technology yana iya detecting wanda yayi attempt zai shige shi da wrong information, kuma ya dakatar da mutum na har abada daga shiga tsarin domin 'dora Coin ko wani information.


Sannan ba'a iya kwace shi zuwa hannun mutum guda, saboda an gina BlockChain Technology ne akan tsaron da wani 'dan Adam ba zai iya chanza shi ba.

Kuma baya karkashin kulawar wata kasa ko wata gwamnati ko wani mutum, wannan shine babban dalilin gwamnatocin kasashe na yaki da BlockChain Technology, saboda basu da iko dashi.

Toh sai dai asalin tsarin Block Chain Technology ba anyi shine saboda harkar kudi ba zalla.

A'a anyi shi saboda duk wata harkar ajiye bayanai ta Online ne a duniya, sai dai harkar kudin Crypto Currency ta sanya mutane da dama basu san cewa blockchain Technology bai tsaya akan harkokin kudi kadai ba.


Menene Crypto currency?

Crypto Currency kudi ne dake internet, wanda ake mu'amala dashi daga 2009 shekaru 14 da suka wuche zuwa yanzu.

Sai dai, kafin a fara wannan harkar Crypto currency a yau, tun da dadewa, wuraren 1980, masana harkokin internet suke ganin ya dache duniya ta samar ma kanta da harkokin kudaden da ba'a iya ganin su, kuma ba'a iya taba su.

Saboda chigaba da amfani da kudaden takarda yana 'kara karya tattallin arziki duniya.


Ta yadda gwamnatochi suke kashe kudade masu yawa wurin buga su, da kashe kudade masu yawa wurin kula dasu idan sun yage ko sun 'kode ko sun lalache, sannan ana saurin sache su da gano inda suke da wanda yake dasu.

Wannan yana daga chikin a baben da suka sa manyan masana ganin an kawo karshen wannan matsalar.

Tun daga lokachin da aka fito da tsarin transfer din kudi ta waya, daga Account din mutum na banki zuwa wani banki masana suka tabbatar da chewa tsarin BlockChain Technology zai yi nasara.

Kuma hakan aka yi, gashi yayi nasara.


Har wa yau, tun shekarun baya masu kokarin kwato 'yanchin 'dan Adam suna chewa ya kamata ache a yanzu mutane sun samu "Financial Freedom" wato " 'Yanchin gashin kai ta bangaren harkokin kudi", ba sai sun jira wata kasa ko wata gwamnati ta aminche da kudi su ba.

Suna chewa saka bakin gwamnati achikin harkar kudi yana danne chigaban duniya da walwalar mutane.

A shekarar 1985 wani Baturen kasar America masanin harkar internet yayi yunkurin samar da kudin Online mai kama da Crypto Currency na yanzu, sai dai kasar Amurka ta kama shi, ta daure shi, daga bisani aka yi zargin ta hallakar dashi.


A 1997 wani 'dan kasar Japan ya sake irin wannan yunkurin na samar da kudin Online amma kasar Japan ta kama shi, haka dai abun ya chigaba da tafiya tsakanin masu neman "Financial Freedom" da gwamnatocin kasashe.

A shekara ta 2008 wani masanin harkar internet kuma 'dan rajin neman Financial Freedom a duniya, wanda akache sunan sa "Satoshi Nakamoto", yayi nasarar kera kudin Online, kuma ya saka masa suna "Bitcoin".


Bayan ya kammala aikin a 2008, sai a 2009 ya qaddamar dashi, wanda shine yayi nasara a karon farko a tarihin duniya da har aka gagara dakatar dashi.

Sai dai anche Satoshi Nakamoto ya gina aikin sa ne akan wanda 'dan kasar Japan din nan ya faro.

Har yanzu ba'a san fuskar Satoshi Nakamoto ba, sai dai bincike ya nuna chewa suna ne irin na 'yan kasar Japan.


Kudin farko da aka samar shine "Bitcoin", an saka masa sunan ne saboda an gina lissafin na'urar juyawa kudin ne da lissafin Computer na salon Algorithm, wato shi Algorithm asalin wanda ya kirkiro wannan lissafin da Computer take kai wani babban Malamin Musulunci ne, sunan "Imam Jabir Bin Hayyan Al-Khawarizmi", shine Turawa suka boye sunan sa domin kada duniya tasan Musulmi ne suka kawo wannan tsarin lissafin na Computer.

Tsarin lissafin algorithm akan Computer yana bugawa ne da 'digo ko "Bit".


Toh daga nan suka saka sunan kudin Crypto currency na farko da "Bitcoin", shi Bitcoin a yau (27-08-2023) yana Naira miliyan 20,128,493.37 a kudin Nigeriya.

Amma a farkon lokacin da aka kirkiro shi yana Naira biyar, ko Naira goma a 2009, bayan shekaru 10 ya tashi daga Naira goma ya koma Naira miliyan 24 ko wane daya, misali: wanda ya sayi Bitcoin guda dari a 2009 a yau kana ganin nawa yake dashi? ai da yawa.


Bitcoin ba shine Crypto Currency ba, shi Bitcoin 'daya ne daga chikin kudaden da suke yawo online kuma ake amfani dasu, shi Bitcoin dai shine na farko, shine babba dan haka yafi kowane Coin tsada.

Misali:

Idan aka che maka akwai kudaden Takarda a duniya (Fiat Currency) a duniya da yawa, toh kudin Nigeriya (Naira) ba itache kadai kudin da ake amfani da ita a duniya ba.

.

Akwai Riyal, akwai Dollar, akwai Cefa, akwai Ghana Cedi, akwai Pound, akwai Yuro da sauran su.

Toh haka ma Crypto currencies suke, akwai su da yawa sun fi dubu uku akan Block Chain Technology na duniya, misali, akwai:

1. Bitcoin.

2. Etherium.

3. Litecoin.

4. Binance (BNB).

5. Doge coins.

6. Tron (TRX).

7. ADA, Cardano.

8. Steem, Hive, XRP, HOT, BitTorrent......

.

Zan tsaya a nan, a wannan rubutun nawa.

 Nasan yanzu dai anfahimchi mene Crypto CUrrency idan allah yabani dama da tsawon rai zanyi bayani nagaba abinda dai yasamu daga chikin ilimin da allah yabani ngd mai magana naku Omaro, kukasanche tare damu domin chigaba da fadakarwa da kuma ilimantarwa.

Allah yasa mu dace.



Post a Comment

1 Comments