RABE-RABEN KASUWANCHIN CRYPTO CURRENCY
FROM [ CRYPTO WORLD ]
Akwanakin baya munyi bayani akan ma'anar CRYPTO CURRENCY yau kuma insha allah zanyi bayani gameda RABE-RABEN KASUWANCHIN CRYPTO CURRENCY dayardar allah idan allah yabamu iko.
Kasuwar CRYPTO takasasu kashi-kashi har kashi guda biyar wayanda insha allah zamu bayaninsu daki-daki insha allah.
1. HOLDING
2. SWINGING
3. DAY TRADING
4. SCALPING
5. ARBITRAGE
1. HOLDING:- Holding wani kashi ne na sana'ar Crypto Currency wanda ake siyan kaya a ajiye su su yi watanni ko shekaru ba tare da an siyar da su ba.
Wannan yana daya daga chikin kasuwanchin Crypto masu kawo kudi a wannan bangaren domin zaka ga mutum ya sayi kananun Coins/Tokens guda miliyoyi a farashin da bai fi N30,000 ba amma idan suka yi shekara daya ko biyu sai kaji ana chewa sun kai Miliyoyi.
Yana da kyau ko baka irin wannan kasuwanchin ka ringa siyan kananun coins na kudi kadan kana ajiyewa.
2. SWINGING:- Wannan ma wani tsari ne wanda mafi yawanchin mutane suke yin shi. Ana siyan Coins ne sannan a siyar dasu chikin yan kwanaki ko satittika daga suntashi ko yayane.
3. DAY TRADING:- Wannan kuma ana siyan Coins ne sannan a siyar da shi a ranar da aka siye shi ba tare da barin shi ya kwana ba. Wannan kasuwanchin yafi yawa ga matsorata wadanda suke tsoron kada suyi asarar kudin su, sannan kuma yana da hadarin da zasu iya yin asara domin suna duba lokachin da kasuwa take yin kyau ne kawai sai su sayi Coins wanda idan kasuwar ta tsaya zasu iya yin asara a ranar.
4. SCALPING:- Anan kuma idan aka sayi coins ana sayar dashi ne yan mintuna ko sakanni, ma'ana idan aka ga coins yana wuta sai a siya, daga ya dan tsaya sai a chire.
Wasu lokutan masu irin wannan kasuwar suna iya siyan coin yayi kasa ba tare da sun mayar da ko kudin da aka chaje su ba balle kuma riba.
5. ARBITRAGE TRADING:- ARBITRAGE TRADING ya kasu kashi uku:-
1. Yadda ake amfani da ATM a sayi Coin da farashi mai sauki.
2. Yadda ake siyan Coin a wata Exchanger a sayar a wata a sami riba.
3. Yadda ake siyan Coin ta wata hanya ta P2P a juya shi a sayar a sami riba nan take.
Achikin dukkan nin wayan nan hanyoyi ana samun alkhairai masu tarin yawa sosai da sosai wasu lokutanma idan allah yayi arzikinka awajan shikkenan kasha kwana allah yasa mudache ameen
From Omaro
0 Comments